in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Israila ta jikkata Falastinawa masu zanga zanga 109 a kan iyakar zirin Gaza
2018-05-26 17:12:47 cri
Kamfanin dillancin labaran Falastinu na WAFA ya bada rahoton cewa, sojojin Isra'ila sun jikkata Falastinawa masu zanga zanga akalla 109 ta hayar harbin bindiga a jiya Juma'a, a lokacin da suka yi arangama da su a kan iyakar zirin Gaza.

Daga cikin wadanda suka samu raunuka, akwai mata 9, da kananan yara 4, kana 3 daga cikinsu sun samu raunuka masu tsanani, bayan da sojojin Isra'ila suka harbesu a kai, yayin da ragowar mutanen suka samu kananan raunuka.

Duk da irin yanayi zafi da ake fama da shi a lokacin azumin watan Ramadan, wata mai tsarki wanda al'ummar musulmi ke gudanar da ibadun azumi, Falastinawa na cigaba da yin zanga zanga a yankunan dake kan iyakar zirin Gaza.

Sama da Falastinawa 120 ne aka hallaka, kana an jikkata dubbai, a yayin da jami'an tsaron Isra'ila suka bude wuta kan dandazon Falasdinawa dake zanga zanga kan iyakar zirin Gaza a ranar 30 ga watan Maris.

Su dai al'ummar Falastinawa suna zanga zangar neman hakkokinsu ne na matsugunansu da yahudawa 'yan kama wuri zauna suka mamaye mai dadadden tarihi tun daga shekarar 1948. (Ahmad)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China