in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Isra'ila ta tarwatsa tashoshi soja guda uku na Hamas dake yankin Gaza
2018-05-17 13:41:27 cri
A jiya ne rundunar tsaron Isra'ila ta sanarwa da cewa, sojin Isra'ila sun tura tankin yaki sau biyu don su tarwatsa wasu tashoshin sintiri guda uku na kungiyar Hamas dake zirin Gaza.

Rundunar Isra'ila ta ce, harin da aka kai a wannan karo mayar da martani ne kan harin da Hamas ta kaiwa sojojin Isra'ila da aka jibge a iyakar Gaza, sai dai kuma babu wani sojan Isra'ila da ya ji rauni sakamakon wannan hari.

Rahotanni na cewa, yanayi na kara tsanantawa tsakanin Palasdinu da Isra'ila. A ranar 14 ga wata ne dai Amurka ta sanar da bude ofishin jakadancinta dake Isra'ila a birnin Kudus, lamarin da ya haifar da barkewar zanga-zangar a birane da dama na Palasdinu a wannan rana, inda masu zanga-zanga suka yi arangama da sojin Isra'ila, abin da ya haddasa rasuwar Palasdinawa fiye da 60 yayin da wasu 3000 suka ji rauni. (Amina Xu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China