Firaministan Isra'ila Benjamin Netayahu, ya bayyana a jiya yayin taron ministocin kasar cewa, Isra'ila za ta hana Iran kara jibge makamai a Sham.
Ya ce, a cikin watannin da suka gabata, rundunar IRGC ta Iran ta jigbe wasu makamai na zamani a kasar Sham don kai hari kan Isra'ila, ciki hadda jirgin sama maras matuki da makamai masu linzami da dai sauransu. A cewarsa, Isra'ila ba ta son tsananta halin da ake ciki a yankin, amma ta yi shiri tsaf don mayar da martani, ya ce, Isra'ila za ta yi iyakacin kokarin hana matakin sojan da Iran za ta dauka kanta, duk da cewa za a tada wani yaki tsakaninsu.
Ban da wannan kuma, Netayahu ya shedawa manema labarai bayan taron cewa, yarjejeniyar nukiliyar Iran ba ta da kyau ko kadan, kuma ya kamata a gyara ta duka ko hana aiwatar da ita baki daya, idan ba haka ba, Iran za ta kafa wani sansanin makaman nukiliya cikin gajeren lokaci.(Amina Xu)