in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi bikin kide-kide cikin jirgin kasa mai sauri samfurin Fuxing
2018-05-23 16:06:21 cri

Jiya Talata da yamma, masu fasahar kayan goge na Violin, na babban dakin wasan kwaikwayo na kasar Sin, da mawaka na kungiyar gabatar da wasannin kide-kide da raye-raye ga ma'aikatan jirgin kasa, sun shiga jirgin kasa mai saurin tafiya sosai samfurin Fuxing, inda suka yi karamin bikin kide-kide ga fasinjojin jirgin kasan Fuxing mai lambar C2061, da kuma mai lambar C2230.

Bikin ya gamsar da fasinjoji kwarai da gaske. Wasu sun bayyana cewa, gaskiya wannan ne karo na farko da suka kalli bikin kide-kide cikin jirgin kasa mai sauri, wanda ya burge su kwarai da gaske. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China