Ita ma hukumar raya kasa da yin gyare-gyare ta kasar Sin ta yi hasashen cewa, daga ranar 1 ga watan Fabrairu zuwa 12 ga watan Maris na wannan shekara za a yi zirga-zirga kimanin biliyan 2.98, wato daidai da alkaluman shekarar da ta gabata.
Daruruwan miliyoyin Sinawa ne dai suke komawa garuruwansu domin murnar bikin Bazara bisa kalandar gargajiyar kasar Sin tare da iyalansu. (Ibrahim Yaya)