in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta cimma burinta a fannin zuba jari a bangaren jiragen kasa
2018-01-02 12:11:33 cri
Hukumomi a kasar Sin sun bayyana cewa hasashen da kasar ta yi na samu bunkasuwa ta fuskar juba jari a fannin sufurin jiragen kasa ya cika ma'aunin hasashen da aka yi cikin shekarar 2017 data gabata.

Sin ta kashe yuan biliyan 801, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 123 wajen gudanar da aikin gina sabbin layukan dogo mai nisan kilomita 3,038 wadanda tuni suka fara aiki a shekarara ta 2017, inda kasar ta cimma hasashen da ta yi na zuba jarin yuan biliyan 800 a fannin samar da sabbin layin dogon mai adadin kilomita 2100, kamar yadda hukumar kula da sufurin jiragen kasa ta kasar Sin ta sanar.

Zuwa karshen shekarar ta 2017, kasar Sin ta samar da layin dogon kimanin kilomita 127,000.

Daga cikin adadin, akwai na jiragen kasa mai saurin tafiya kimanin kilomita 25,000 daga adadin kilomita 22,000 da ake dasu a karshen shekarar 2016.

Ministan sufurin kasar Sin Li Xiaopeng, ya bayyana cewar kasar Sin ta cimma hasashen data yi a harkar sufuri wandada ta kuduri aniyar aiwatar zuwa shekarar 2018.

Ya ce nan da shekaru uku masu zuwa, fannin sufurin zai taka muhimmiyar rawa wajen kawar da talauci da kuma samar da gagarumin cigaban kasar.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China