in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An samu karuwar tafiye-tafiye ta jiragen kasa yayin hutun sabuwar shekarar 2018
2018-01-01 12:04:09 cri
Sama da matafiya miliyan 11.29 ne suka yi zirga zirga ta jiragen kasa a cikin kasar Sin a ranar Asabar, rana ta farko a jerin kwanaki 3 da za a shafe ana hutun maraba da sabuwar shekarar 2018.

Wasu alkaluma da kamfanin sufurin jiragen kasa na kasar Sin ya fitar a ranar Lahadi, sun nuna cewa adadin matafiyan ya karu da sama da kaso 16.4 bisa dari, idan an kwatanta da na watan farko na shekarar 2017 da ta gabata.

Alkaluman kamfanin sun kuma nuna cewa, ana sa ran fasinjoji kusan miliyan 8.5 za su yi zirga-zirga ta jiragen na kasa a ranar Lahadi, kuma tuni aka kara wasu jiragen kasan wucin gadi guda 155 domin biyan bukatun fasinjoji.

Kaza lika kamfanin ya yi hasashen cewa, tsakanin ranekun Juma'a da Litinin, yawan tafiye-tafiye da fasinjoji za su yi ta jiragen kasa zai kai miliyan 37, adadin da zai haura na bara da kusan kaso 7 bisa dari.

Adadin tafiye-tafiye zuwa sassan kasar Sin mafi yawa da aka taba samu, shi ne na ran 1 ga watan Oktobar bara, wanda ya kai zirga zirga miliyan 15.03. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China