Lu ya ce, yawan layukan dogo masu saurin tafiya da ake amfani da su a kasar a karshen shekarar 2017 sun kai kaso 66.3 cikin 100 na yawan layukan da ake amfani da su a duniya.
A cewarsa, jarin da ake fatan zubawa a bangaren sufurin jiragen kasa a shekarar 2018, zai kai yuan biliyan 732, kwatankwacin dala biliyan 112, adadin da ya yi kasa da matsakaicin jarin da aka zuba daga shekarar 2013-2017. Ya ce a wannan shekarar, hukumar tana shirin gina sabbin layukan dogo, kuma daga cikin wannan adadi kilomita 3,500 za su kasance masu saurin tafiya ne.
Jami'in ya kara da cewa, kasar Sin tana fatan gina kilomita dubu 175 na layukan dogo nan da shekarar 2025, idan aka kwatanta da kilomita dubu 127 da ke aiki a karshen shekarar 2017 da ta shude.
A shekarar 2017, fasinjoji biliyan 3.04 ne suka yi zirga-zirga ta jiragen kasa, karin kaso 9.6 cikin 100 bisa makamancin lokaci na bara. Kuma sama da kaso 56 cikin 100 na zirga-zirgar an yi su ne ta jiragen kasa masu saurin tafiya. (Ibrahim Yaya)