in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin za ta samar da jirgin kasa mai gudun kilomita 400 cikin sa'a guda
2018-02-27 10:07:34 cri

Kwararre a fannin fasahar kera jirgin kasa mai saurin tafiya na kasar Sin, Ding Rongjun ya bayyana yayin wani taron ganawa da manema labaran da aka shirya jiya Litinin cewa, kasarsa na kokarin samar da jiragen kasa masu sauri da gudunsu ya kai kilomita 400 cikin sa'a guda.

Ding Rongjun, ya kara da cewa, kasar Sin na gudanar da bincike domin samar da wani sabon jirgi mai aiki da karfin maganadisu da zai rika gudun kilomita 600 cikin kowace sa'a.

Ya ce, a yanzu, sun mayar da hankali kan yadda za su hada talabijin a cikin jiragen, ta yadda fasinjoji za su iya kallo fina-finai a jikin alluna tagogi, yana mai cewa, a nan gaba, za a yi amfani da fahasar dake aiki kai tsaye, wadda ba ta bukatar bil adama.

Matakin karshe na gudun jiragen kasa na kasar Sin ya kai kilomita 350 cikin sa'a guda ne a lokacin da jiragen suka fara zirga-zirga tsakanin biranen Beijing da Shanghai, a ranar 21 ga watan Satumban 2017. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China