in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sama da tafiye-tafiye miliyan 100 aka yi ta jirgin kasa a lokacin hutun kasa na kasar Sin
2017-10-08 12:27:36 cri
kamfanin kula da sufurin jiragen kasa ta kasar Sin ta ce jiragen kasa sun fuskanci yawan hada-hadar jama'a a lokacin hutun kasa da aka yi, inda suka yi ta jigilar mutane masu yawon bude ido ko wadanda ke komawa gida dan saduwa da iyalansu kafin su kuma komawa makaranta ko wuraren aikinsu.

Hukumar ta ce kimanin al'ummar kasar miliyan 105 ne suka yi amfani da jiragen wajen yin bulaguro tun bayan da aka fara samun tururuwan matafiya a ranar 28 ga watan Satumba.

A bana, an tsawaita ranakun hutun zuwa 8 domin bikin ranar tsakiyar kaka da ake kira da Moon Cake Festival da ya fado a ranar 4 ga watan Oktoba.

Mutane kimanin miliyan 12.4 ne suka yi bulaguro a ranar Jumma'a, adadin da ya karu da kaso 8.6 idan aka kwatanta da bara, inda ranar ta kasance rana ta 7 a jere da a kulla yaumin ake tafiye-tafiye sama da miliyan 10 ta jiragin kasa.

Ko ajiya Asabar an yi hasashen yin tafiye-tafiye miliyan 13.6, inda kamfanin ya ce ya shirya karin jirage 911 domin tabbatar da komai ya gudana lami lafiya.

Hanyoyin sufurin jiragen kasa na kasar Sin sun kafa wani sabon tarihi ta fuskar fasinjojin da suke samu a kullum, inda a ranar 1 ga watan Oktoba da ta kasance ranar farko ta hutun na kwanaki 8, aka yi kimanin tafiye-tafiye miliyan 15.

Wani hasashe da kamfanin ya yi kafin lokacin hutun, ya bayyana cewa jiragen kasa za su yi jigilar fasinjoji 130 cikin ranaku 11 da za biyo bayan ranar 28 ga watan Satumba. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China