Mr. Dujarric ya ce, babban magatakardan MDD Antonio Guterres ya mika sakon ta'aziyya ga al'ummomi da gwamnatin kasar Bangladesh.
A 'yan shekarun nan, ana ci gaba da samun tashe-tashen hankula a kasar Afirka ta Tsakiya, musamman ma hare-haren da ake tsakanin dakaru masu dauke da makamai na kungiyar Anti Balaka da tsoffin mambobin kungiyar Seleka, lamarin da ya haddasa dimbin fararen hula su zama 'yan gudun hijira.
A halin yanzu kuma, ana ci gaba da fama da tashe-tashen hankula a kasar, ciki har da rikice-rikicen da ake tsakanin kabilu daban- daban, da kuma hare-haren da ake kai wa sojoji masu kiyaye tsaron kasar. (Maryam)