in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
WHO: Yaduwar cutar Ebola a Congo-Kinshasa ba ta kai matsayin "yanayin kiwon lafiya na gaggawa na duniya" ba
2018-05-19 16:27:07 cri
A ranar 18 ga wata, hukumar lafiya ta duniya wato WHO ta sanar da cewa, barkewar cutar Ebola a kasar Congo-Kinshasa ba ta kai matsayin tsarin kiwon lafiya na gaggawa wadda kasashen duniya suke mai da hankali a kai ba. Hakan ne ya sa, a halin yanzu, babu bukatar a hana yawon shakatawa da harkokin ciniki zuwa kasar Congo-Kinshasan.

Hukumar WHO dai ta kira taron gaggawa game da yaduwar cutar Ebola a kasar, inda aka tsai da kuduri daga matsayin kalubalen yaduwar cutar Ebola a kasar Congo-Kinshasa daga "babban matsayi" zuwa "matsayi mai matukar girma", yayin da daga matsayin kalubalen yaduwar cutar Ebola a kasashen dake kewaye daga "matsakaici" zuwa "babba", kana, kalubalen yaduwar cutar a kasashen duniya ya ci gaba da kasancewa a matsayin "karami".

Mataimakin shugaba mai kula da ayyukan gaggawa na hukumar WHO Peter Salama ya bayyana cewa, ya zuwa ranar 17 ga wata, an riga an gano mutane 45 wadanda mai iyuwa ne sun kamu da cutar, ciki har da mutane 14, wadanda aka tabbatar da kamuwarsu. Daga cikin mutane 25 da suka rasu, an tabbatar da mutum 1 ya rasu sakamakon kamuwa da cutar Ebola.

A halin yanzu, hukumar WHO ta riga ta tura masana zuwa kasar, kuma an riga an isar da allurar rigakafi na gwaji zuwa birnin Kinshasa a ranar 16 ga wata. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China