in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Adadin yawan mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar Ebola ya karu zuwa 11 a Jamhuriyar Demokuradiyyar Kango
2018-05-11 09:58:57 cri
Ministan kiwon lafiya na Jamhuriyar Demokuradiyyar Kango, Orly Ilunga ya sanar a daren jiya Alhamis cewa, kawo yanzu, adadin yawan mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar Ebola a jihar l'Equateur dake arewa maso yammacin kasar ya kai 11. Haka kuma akwai wasu ma'aikatan jinya wadanda suka kamu da cutar sakamakon barkewar Ebola a wannan karo, lamarin da ya janyo matukar damuwa a kasar.

Orly Ilunga ya bayyana a wajen taron manema labarai cewa, baya ga cutar Ebola, akwai barkewar sauran wasu masassara a kasarsa. Game da mutanen da suka rasa rayukansu a kwanan baya, wadanda ake zargin su sun kamu da cutar Ebola kuwa, ministan ya ce, ba za'a iya tabbatar da musabbabin mutuwarsu ba, sai dai bayan an yi gwajin jinin su. (Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China