in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Cutar Ebola ta sake bullowa a Kongo Kinshasa
2018-05-09 13:19:44 cri

Hukumar kiwon lafiya ta kasar Kongo Kinshasa ta tabbatar da sake barkewar mumunar cutar Ebola a kasar, inda ake tsammanin mutane 21 sun kamu da ita, yayin da aka tabbatar da mutane 2 daga cikinsu. Ministan lafiya na kasar Orly Ilunga ya yi sanarwa a jiya cewa, ana tsammanin mutane 21 dake jihar Equatorial na arewa maso yammacin kasar sun kamu da cutar, inda 17 daga cikinsu suka rasa rayukansu. Karkashin taimakon hukumar kiwon lafiya ta duniya WHO da kungiyar likitoci ta Doctors Without Borders, an tattara sakamakon bincike 5, inda aka tabbatar da mutane 2 daga cikinsu sun kamu da cutar.

Orly Ilunga ya ce, gwamnatin kasar ta riga ta tura masana da kayayyaki domin tinkarar cutar a wannan sabon zagaye.

Hakazalika, WHO ta sanar a jiya cewa, ta lura da cewa, Kongo Kinshasa na fuskanta barkewar cutar Ebola, kuma ta tura masana don ba da taimako ga gwamnatin kasar, wajen dakile yaduwar cutar. (Amina Xu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China