Babban daraktan WHO Dr. Tedros Adhanom Ghebreyesus, na shirin ziyartar kasar cikin karshen makon nan, domin duba halin da ake ciki, ya kuma bada umarnin ci gaba da gudanar da ayyukan jin kai, karkashin tsare tsaren kiwon lafiyar da hukumomin kasar ke aiwatarwa.
Wasu alkaluma sun nuna cewa, ya zuwa ranar Juma'a, yawan wadanda ake zaton sun kamu da cutar Ebola a kasar a tsakanin makwanni 5 sun kai mutum 34, ciki hadda mutum 2 da aka tabbatar suna dauke da cutar, da 18 da suka riga suka rasu ake kuma zaton cutar ce ta hallaka su, sai kuma wasu 14 da ba a riga an tabbatar da kamuwar su ba tukuna.
Kaza lika an dauki jinin wasu mutanen 5, inda aka samu 2 daga cikin su na dauke da cutar ta Ebol, a bayan gudanar da gwaje gwaje a dakin bincike. (Saminu Hassan)