Alkaluman kididdigar hukumar WHO na nuna cewa, daga ranar 4 ga watan Afrilu zuwa 13 ga watan Mayu, an samu rahoton mutane 39 da aka tabbatar ko ake zargin sun kamu da cutar Ebola, a kalla mutane 18 daga cikinsu sun mutu.
Yankin da cutar ta barke a wannan karo wato yankin Bikoro dake jihar Equateur yana kusa da arewa maso yammacin iyakar kasar.
Wannan ne karo na 9 da aka samu bullar cutar Ebola tun bayan da aka fara gano cutar a kasar Congo Kinshasa a shekarar 1976 a karon farko. Hukumar WHO ta ayyana kasar da kasashen dake kewayenta a matsayin matsakaicin kasashe masu tinkarar kalubalen cutar Ebola, da yin hadin gwiwa tare da kasashen wajen sa ido kan cutar da shirya tinkarar hadarin bazuwar cutar tare. (Zainab)