A ranar Laraba ne majalisar zartarwar kasar, ta umarci ma'aikatar lafiyar da ta inganta matakan sa ido, domin tunkarar yuwuwar barkewar Ebola a kasar.
Da yake ganawa da manema labarai jiya, a Abuja babban birnin kasar, Isaac Adewole, ya ce umarnin na majalisar zartarwar, ya biyo bayan rahoton barkewar cutar a Jamhuriyar Demokradioyyar Congo.
A nata bangaren, Kakakin hukumar kula da filayen jiragen saman kasar (FAAN) Henrietta Yakubu, ta shaidawa Xinhua cewa, har yanzu, hukumar na da kayakin aiki da isassun jami'ai a filayen jirgin sama domin kare cutar daga shiga kasar. Ta ce hukumar ba za ta yi kasa a gwiwa ba, a kokarin da take na tabbatar da binciken dukkan fasinjoji masu shiga kasar yadda ya kamata a filayen jirgen sama. (Fa'iza Msutapha)