in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministan harkokin wajen Iran zai kai kawo ziyara nan kasar Sin
2018-05-13 16:16:49 cri
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang, ya bayyana a jiya Asabar cewa, bisa gayyatar da ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya yi masa, ministan harkokin wajen kasar Iran Mohammad Javad Zarif, zai fara ziyarar aiki a nan kasar Sin a yau Lahadi.

Geng Shuang ya ce, a wannan karo, Mr. Zarif zai ziyarci kasashen Sin, da Rasha da wasu kasashen Turai, domin yin musayar ra'ayoyi kan batun makamashin nukiliyar kasar Iran. Kuma kasar Sin na daya daga cikin wadanda suka kulla yarjejeniyar batun makamashin nukiliyar kasar Iran, shi ya sa tana mai da hankali sosai kan wannan batu.

A sa'i daya kuma, Sin tana fatan gudanar da shawarwari da dukkan kasashen da batun nukiliyar kasar Iran din ya shafa, ciki har da ita kanta kasar ta Iran. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China