in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rasha ta yi kira ga Isra'ila da Iran su yi shawarwari
2018-05-11 09:28:45 cri
Sakatare mai kula da batun yada labarai na shugaban kasar Rasha Dmitri Peskov, da ministan harkokin wajen kasar Sergei Lavrov, da mataimakinsa Bogdanov, a jiya Alhamis 10 ga wata sun yi kira ga Isra'ila da Iran da su yi hakuri da juna, su kuma gudanar da shawarwari don kawo karshen rashin fahimtar juna dake tsakaninsu.

Kakakin rundunar tsaron kasar Isra'ila Jonathan Conricus ya bayyana a wannan rana cewa, da daren ranar 9 ga wata, da kuma safiyar 10 ga wata, rundunar soja ta Iran ta "Quds Force", ta harba rokoki kimanin 20 daga sansaninta dake kasar Sham, zuwa ga tuddan Golan dake karkashin ikon Isra'ila, daga bisani kuma sojojin Isra'ila suka kaddamar da hari kan na'urorin da Iran ta jibge a kasar Sham. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China