in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rasha ta yi kira ga kasashe masu alaka da yarjejeniyar nukiliyar Iran da su ci gaba da martaba yarjejeniyar
2018-05-11 13:46:42 cri

Ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergei Lavrov ya bayyana jiya Alhamis a Moscow cewa, Rasha na mai da hankali sosai kan janyewar Amurka daga yarjejeniyar nukiliyar Iran, kuma ta yi kira ga kasashe da suka sa hannu kan wannan yarjejeniya da su kara shawarwari da juna don ganin ba a yi watsi da ita ba.

Wani rahoto da shafin yanar gizo na ma'aikatar harkokin wajen kasar ta Rasha ya wallafa ya nuna cewa, Sergei Lavrov ya zanta da manema labarai bayan ya gana da takwaransa na kasar Jamus Heiko Maas, inda ya bayyana cewa, yarjejeniyar na da babbar ma'ana wajen tabbatar da zaman lafiya a yankin yammacin Asiya da hana yaduwar makaman kare-dangi. Kana Rasha ta nuna damuwa sosai kan janyewar Amurka daga wannan yarjejeniya, a ganinta, matakin da Amurka ta dauka ya sabawa kuduri mai lamba 2231 na kwamitin sulhu na MDD. Ya ce, ya kamata kasashe masu ruwa da tsaki su nazarci sakamakon janyewar Amurka, kuma su yi shawarwari tare da daukar matakan da suka dace ta yadda za a ci gaba da martaba yarjejeniyar. (Amina Xu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China