in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Majalisar addinin Iran ya jaddada ikon jama'ar kasa kan raya makamashin nukiliya
2018-05-10 11:17:02 cri
Jiya Laraba, majalisar addinin kasar Iran Ayatollah Khamenei ya fidda jawabi, inda ya sake jaddada cewa, raya makamashin nukiliya iko ne na jama'ar kasa ta Iran. Ya yi wannan jawabi ne biyowa bayan janyewar Amurka daga yarjejeniyar batun nukiliyar kasar Iran, a yayin ganawarsa da malamai da dalibai na wata jami'a. Ya ce, wannan iko na al'ummomin kasa ne, wanda zai kare mutunci da moriyarsu yadda ya kamata.

Haka kuma, ya nuna cewa, makamashin nukiliya ainihin bukatun kasar ne, kuma bayan shekaru da dama, kasar Iran za ta bukaci wutar lantarki misalin Megawatt dubu 20 da makamashin nukiliya zai samar.

Kuma yana ganin cewa, dukkanin takunkumin da kasar Amurka ta kakabawa kasar Iran, da kuma kiyayya da Amurka ta nuna mata, ko kadan ba za su shafi harkokin raya makamashin nukiliya da kasar Iran take yi ba. Ya ce, ko babu wannan batu na nukiliya, Amurka za ta nemi wata hujja ta daban.

Bayan shugaban kasar Amurka Donald Trump ya sanar da janyewar kasarsa daga yarjejeniyar nukiliyar kasar Iran, shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron, da firaministar Birtaniya Theresa Mary May, da takwaranta ta Jamus Angela Dorothea Merkel, sun ba da haddadiyar sanarwar a wannan rana, inda suka yi alkawarin cewa, kasashensu za su ci gaba da bin yarjejeniyar, kuma za su dukufa wajen aiwatar da yarjejeniyar yadda ya kamata. Amma Ayatollah Khamenei ya ce, ba shi da imani kan alkawarin da kasashen uku suka yi. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China