Wannan mataki dai na zuwa ne, yayin da shugaban Amurka Donald Trump, ya ayyana janyewar kasar sa daga yarjejeniyar makamashin nukiliyar Iran.
Wata sanarwa da baitulmalin Amurkan ya fitar, ta ce Amurka da hadaddiyar daular Larabawa, sun amince su yi hadin gwiwa, wajen dakile tasirin musayar kudi da Iran, wanda kafin hakan ke samarwa dakarun rundunar juyin juya halin Iran din ko IRGC-QF miliyoyin dalolin Amurka, kudaden da dakarun ke amfani da su, wajen aiwatar da harkokin su na tallafawa kungiyoyin yankin dake mara masu baya.
Sakataren baitulmalin Amurka Steven Mnuchin, ya jaddada cewa, gwamnatin Iran da babban bankin kasar, na amfani da damar samun musayar kudade ta hadaddiyar daular Larabawa, wajen tallafawa rundunar IRGC-QF. (Saminu)