A cikin wannan sanarwa, Yukiya Amano ya bayyana cewa, bisa yarjejeniyar nukiliyar Iran da aka cimma tsakanin bangarorin daban-daban a watan Yuli na shekarar 2015, Iran tana karkashin cikakken bincike daga IAEA.
A watan Yuli na shekarar 2015, Iran da kasashe shida wato Amurka, Birtaniya, Faransa, Rasha, Sin da Jamus, sun kai ga cimma matsaya daya kan yarjejeniyar nukiliyar Iran.
Bisa wannan yarjejeniya, Iran ta yi alkawarin kayyade shirin ta na makaman nukiliya, tare da amfani da makamashin nukiliyar yadda ya kamata. Hakan ya sa kasashen duniya suka janye takunkumin da suka kakkabawa Iran din.
To sai dai kuma shugaban kasar Amurka Donald Trump ya sanar a ran 8 ga wata cewa, Amurka za ta janye daga wannan yarjejeniya, tare da maido da takunkumi kan Iran. (Amina Xu)