in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
'Yan tawayen Houthi na Yemen sun hallaka Abdallah Saleh da danginsa
2017-12-05 09:15:40 cri
Wani babban kusa a kungiyar 'yan tawayen Houthi ya tabbatarwa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, an kashe tsohon shugaban kasar Yemen Ali Abdullah Saleh, tare da dan wansa da danginsa da kuma babban sakataren jam'iyyar Saleh.

An kashe Saleh da mataimakin babban sakataren jam'iyyar tasa Yasser al-Awadhi ne da safiyar jiya Litinin a lokacin da suke yankin Khawlan dake kudu maso gabashin wajen birnin Sanaa, a lokacin da suke kokarin tserewa zuwa lardin Marib wanda ke karkashin ikon dakarun dake samun goyon bayan kasar Saudiyya.

Shi ma Tarek dan danuwan Saleh, an hallaka shi ne da safiyar ranar Litinin a gidansa dake rukunin gidaje na Haddah a babban birnin kasar Sanaa.

Shi kuwa Arif al-Zuka, sakatare janar na jam'iyyar Saleh shi ma an kashe shi ne a Sanaa.

A halin yanzu, kura ta lafa a tashin hankalin da ake fama da shi a babban birnin kasar Sanaa da kewayensa.

Bugu da kari, dakarun tsaro wanda Saudiyya ke jagoranta suna ci gaba da yin shawagi ta jiragen sama a babban birnin kasar. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China