in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kai hari kan ofishin jakadancin kasar Iran dake Yemen
2017-12-04 10:08:15 cri
Rahotanni daga Sanaa, babban birnin kasar Yemen na cewa, gobara ta tashi a ofishin jakadancin kasar Iran dake Sanaa, lokacin da wani makami da aka harba ya fada kan ofsihin jakadancin, biyo bayan wani fada tsakanin mayakan Houthi da magoya bayan tsohon shugaban kasar ta Yemen Ali Abdullah Saleh.

Wani jami'in tsaro ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, kimanin ma'aikatan ofishin jakadancin Iran 20 ne suke ciki a lokacin da aka kai harin. Wasu bayanai kuma na cewa, an ga gawawwaki sama da 100 zube a kan tituna, baya ga a kalla wasu 'yan tawaye dari 2 daga sassan da ke fada da juna da aka kashe da kuma wasu da dama da suka jikkata yayin fadan da ya barke a kusa da ofishin jakadancin kasar ta Iran.

Sabon fadan dai ya barke ne bayan da Saleh da magoya bayansa suka aukawa kungiyar Houthi, wadda ke adawa da kawancen da Saudiya ke jagoranta, kawancen da ke goyon bayan gwamnatin shugaba Abd-Rabbu Mansour Hadi da kasashen duniya ke marawa baya.

Sai dai kuma Saleh ya bayyana kudurinsa na tattaunawa da shugaban kawancen da nufin sasantawa. Yayin da a hannu guda kuma shugaban Houthi Abdul Malek al-Houthi ya zargi Saleh da cin amana, ta hanyar yakar kawancen da Saudiya ke jagoranta.

Har yanzu dai ba a tabbatar da wanda ya tayar da fadan na jiya ba.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China