in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kaddamar da hanyar jirgin sama ta farko daga arewa maso yammacin kasar Sin zuwa London kai tsaye
2018-05-07 15:46:48 cri

Yau Litinin da karfe 3 da minti 15 na yamma ne wani jirgin sama kirar GS7987 mai dauke da fasinjoji ya tashi daga filin jirgin sama na Xianyang dake birnin Xi'an zuwa birnin London na kasar Birtaniya, lamarin da ya alamta cewa, an kaddamar da hanyar jirgin sama ta farko daga arewa maso yammacin kasar Sin zuwa London kai tsaye.

A kowace ranar Litinin da ta Jumma'a ne jirgin sama zai tashi daga Xi'an da karfe 3 da minti 15 na yamma, yayin da zai sauka a London da karfe 8 na dare bisa agogon wurin. Ta haka an rage tsawon lokacin zuwa London daga Xi'an cikin jirgin sama zuwa awyoyi 11 kawai.

Kaddamar da hanyar jirgin sama daga Xi'an zuwa London ya kyautata karfin lardin Shaanxi a matsayin hanyar yin jigilar kaya ta kasa da kasa, kana kuma ya ba da taimako wajen yin mu'amala a tsakanin Shaanxi da ma duk yankin arewa maso yammacin kasar Sin da kuma kasashen Turai ta fuskar tattalin arziki da ciniki da kuma al'adu. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China