Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying ta sanar da cewa, Theresa Mary May, firaministar kasar Birtaniya za ta kawo ziyarar aiki kasar Sin daga ranar 31 ga watan Janairu zuwa ranar 2 ga watan Fabrairu, bisa gayyatar da takwaranta na kasar Sin Li Keqiang ya yi mata, inda za ta halarci taron shekara-shekara na firaministocin kasashen 2.
Madam Hua wadda ta fadi haka a yau Alhamis a yayin taron manema labaru da aka saba shiryawa a nan Beijing. Ta kuma ce, ziyarar da Theresa Mary May za ta kawo kasar Sin, ita ce ta farko tun bayan da ta zama firaministar Birtaniya, ziyarar da take da muhimmiyar ma'ana wajen raya huldar da ke tsakanin Sin da Birtaniya a sabon halin da ake ciki. (Tasallah Yuan)