A yau Jumma'a kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Lu Kang, ya bayyana a yayin taron manema labaru da aka saba shiryawa a nan Beijing cewa, a cikin rahoton da gwamnatin kasar Birtaniya take fitarwa kowace rabin shekara game da harkokin yankin Hongkong na kasar Sin, ta tsoma baki, ta kuma ba da sharhi ba gaira ba dalili kan batun na Hong Kong, har ma tana kokarin nuna tasirinta kan harkokin Hongkong, ko shakka ya kasance wani abu ne da zai bi ruwa, kana zai jawo kyamar kasar daga jama'ar kasar Sin.
An labarta cewa, a ranar 15 ga wata, gwamnatin Birtaniya ta kaddamar da rahoton rabin shekara kan harkokin Hong Kong, wanda ya zama na 42 da gwamnatin Birtaniya ta fitar. (Tasallah Yuan)