Shugaban kasar Sin Xi Jinping da firaministar Birtaniya Theresa May, sun amince su kara fadada dangantakar dake tsakanin su ta kusan "shekaru 50".
Shugabannin biyu sun amince da hakan ne, yayin wata tattaunawa da suka yi ta wayar tarho, sun kuma yi musayar ra'ayi game da yanayin da ake ciki a Syria, da ma batun cinikayyar kasa da kasa.
Shugaba Xi ya bayyanawa May cewa, akwai bukatar gudanar da sahihin bincike, game da batun zargin da aka yiwa mahukuntan Syria na amfani da guba kan fararen hula, irin binciken da zai samar da sakamako wanda zai samu karbuwa ga kowa. A kuma dauki managartan matakan warware takaddamar kasar ta Syria, ta hanyar siyasa ba tare da wani bata lokaci ba.(Saminu Alhassan)