Rahotanni na cewa, kakakin ofishin firaministar kasar Birtaniya ya bayyana a kwanakin baya cewa, firaminista Theresa May za ta kawo ziyara kasar Sin a bana. Game da wannan batu, Lu Kang ya bayyana cewa, a watan Satumban bara ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da Theresa May a lokacin da ta halarci taron kolin kungiyar G20 da aka gudanar a birnin Hanzhou na kasar Sin, inda shugabannin biyu suka tabbatar da makomar bunkasuwar dangantakar dake tsakanin kasashen biyu. Shekarar bana shekara ce ta cika shekaru 45 da kulla dangantakar diplomasiyya a tsakanin kasashen biyu, Sin tana son hada kai tare da kasar Birtaniya domin kara raya dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare a karni na 21 yadda ya kamata. (Zainab)