in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hassan Rouhani: Amurka za ta yi da-na-sani idan ta janye jiki daga yarjejeniyar nukiliyar Iran
2018-05-07 13:57:47 cri

Hassan Rouhani, shugaban kasar Iran ya bayyana cewa, kasar Amurka za ta yi da-na-sani sosai, idan ta janye jiki daga yarjejeniyar nukiliyar Iran, kuma Iran za ta ci gaba da gudanar da harkokin nukiliya ba tare da jin tsoron komai ba.

Mista Rouhani ya bayyana haka ne jiya Lahadi, cikin jawabin da ya yi a wani gangami da aka gudanar, inda ya ce, kudurin Amurka ba zai canza zaman rayuwar jama'ar Iran ba. A cikin watanni da dama da suka wuce ne gwamnatin Iran ta ba da umurni ga hukumominta da su shiryawa tunkarar matakin da Amurka za ta dauka, inda hukumar makamashin nukiliyar Iran ta fara share fagen daidaita batutuwan da za su biyo bayan janye jiki da watakila Amurka za ta yi daga yarjejeniyar.

A watan Janairun bana ne, shugaba Donald Trump na Amurka, ya sanar da tsawaita lokacin dakatar da sanya takunkumi kan Iran sakamakon batun nukiliya karo na karshe. Ya kuma sanya ranar 12 ga watan Mayu a matsayin wa'adin karshe na yin gyare-gyare kan yarjejeniyar nukiliyar Iran, inda ya yi shelar cewa, idan bai gamsu da gyare-gyaren ba, Amurka za ta janye jiki daga yarjejejniyar. Har ila yau mista Trump ya bukaci kungiyar Tarayyar Turai da majalisar dokokin Amurka da su amince da yin gyare-gyare kan yarjejeniyar nukiliyar Iran, inda za a tanadi hana Iran bunkasa makamai masu linzami a cikin yarjejeniyar. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China