Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar ta Iran Bahram Qasemi, ya ce wancan zargi na Morocco ba shi da tushe bare makama. Kuma Iran ba ta taba shiga sabgar wata kasa ta daban ba.
A ranar Talata ne dai Morocco ta ce za ta yanke huldar diflomasiyya da Iran. A cewar Firaministan kasar Morocco Nasser Bourita, kasar sa za ta kori jakadan Iran daga birnin Rabat, za kuma ta rufe ofishin ta na jakadanci dake birnin Tehran.
Ministan harkokin wajen Moroccon ya kara da cewa, kasar sa tana da kwararan shaidu, dake nuna cewa, Iran ta hannun kawar ta wato kungiyar Hezbollah dake kasar Lebanon, na taimakawa kungiyar Polisario da kudade, da samar da horo, domin kungiyar ta iya kaiwa ga gurgunta tsaro da zaman lafiya a Morocco.