in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
IEAE ta ce babu wata kwakkwarar shaida dake nuna cewa Iran na kera makaman nukiliya
2018-05-02 09:22:49 cri
Hukumar dake sanya ido kan amfani da makamashin nukiya ta MDD, ta jadadda cewa, babu wata shaida mai kwari dake nuna cewa Iran na kera makaman nukiliya tun bayan shekarar 2009.

Hukumar ta bayyana haka ne cikin sanarwar da ta fitar a jiya Talata game da batun nukiliyar Iran, inda ta ce ta rufe bincike kan batun.

Sanarwar na zuwa ne bayan Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu, ya gabatar da wasu takardu cikin wani shirin talabijin a ranar Litinin da ta gabata, wadanda ya yi zargin hukumar kasar ta liken asiri, ta samo daga ma'ajiyar adana bayanan nukiliya ta sirri mallakar Iran, yana mai cewa takardun sun tabbatar da Iran na kera makaman nukiliya a boye.

A jiya ne kuma, Ministan harkokin wajen Iran ya yi watsi da zargin na Netanyahu, wanda ya ce na da nufin yin tasiri kan matakin da Shugaban Amurka Donald Trump ke son dauka a baya-bayan nan, game da yarjejeniyar nukiliyar Iran da aka cimma a watan Yulin 2015. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China