Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Rasha, Maria Zakharova ce ta bayyana haka a jiya Alhamis, yayin wani taron manema labarai, inda ta ce manyan jami'an biyu za su gana ne a gefen taron ministocin wajen Rasha da Iran da Turkiyya game da Syria da zai gudana gobe a Moscow.
A cewarta, yayin tattaunawar, za a yi musayar ra'ayi game da batutuwan da suka shafi kasa da kasa da yankuna, ciki har da yadda batun aiwatar da kunshin yarjejeniyar nukiliyar Iran ke kara shiga mummunan yanayi.
Maria Zakharova, ta ce Rasha ta damu ainun da jawaban da shugaban Amurka Donald Trump da takwaransa na Faransa Emmanuel Macron su ka yi a baya-bayan nan game da yarjejeniyar nukiliyar Iran.
Ta ce yarjejeniyar ta cimma daidaito wadda ta kiyaye dukkan muradun wadanda suka amince da ita. (Fa'iza Mustapha)