in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ya kamata a ci gaba da kiyaye cikakkiyar yarjejeniyar nukiliyar Iran daga dukkanin fannoni
2018-04-27 19:28:43 cri
A yayin taron manema labarai da aka yi a Beijing a yau Jumma'a, mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin, Madam Hua Chunying ta ce, kasar Sin tana ganin cewa, kamata ya yi bangarori masu ruwa da tsaki su karfafa shawarwari da musanyar ra'ayi tsakaninsu dangane da halin da yarjejeniyar nukiliyar Iran take ciki, a kokarin ci gaba da kare yarjejeniyar daga dukkanin fannoni.

Jiya Alhamis ne, mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Rasha ya ce, kasarsa ta bayyana damuwa sosai kan ra'ayoyin da shugabannin kasashen Amurka da Faransa suka nuna kwanan baya dangane da yarjejeniyar nukiliyar Iran. Rasha ta sake nanata cewa, bai kamata a sauya ko kuma a kara saka wani abu a cikin yarjejeniyar ba.

Madam Hua ta ce, kasar Sin na fatan ci gaba da kokarin ganin an kiyaye gami da aiwatar da yarjejeniyar daga dukkanin fannoni. (Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China