in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Iran: Babu yiwuwar sake shawarwari kan yarjejeniyar nukiliya kan Iran
2018-05-04 11:02:14 cri

A jiya ne ministan harkokin wajen kasar Iran Mohammad Javad Zarif ya jaddada matsayin Iran game da yarjejeniyar nukiliyar kasar, inda ya bayyana cewa, Iran za ta mayar da martani ga Amurka, da zarar ta fice daga wannan yarjejeniya ko ta ci gaba da saba mata.

Zarif ya bayyana ta Intanet cewa, sakamakon rashin jin dadi da shugaban Amurka Trump ya nuna kan wannan yarjejeniya, har wasu kasashen Turai sun amince su cimma matsaya da Amurka.Wadannan kasashen sun shirya cimma wata sabuwar yarjejeniya, amma abubuwan da suka tattauna, an riga an yi watsi da su kafin a sa hannu kan yarjejeniyar nukiliya ta Iran.

Zarif ya ce, Iran ba za ta mika ikon tabbatar da tsaron kasar a hannun wasu kasashe ba, balle ta ba da damar sake yin shawarwari kan wannan yarjejeniyar da aka riga aka aiwatar da ita ko kara wasu ayoyi a cikinta.

Ya ce, Iran za ta mai da martani ta hanyar da ta dace, idan har Amurka ta ci gaba da saba yarjejeniyar ko ma ta fice daga cikinta. (Amina Xu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China