Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Iran Bahram Qasemi, ya karyata rahoton a lokacin taron kwamitin UNHRC na baya bayan nan a Geneva, wanda kwamitin MDDr ya bukaci a tsawaita wa'adin shirin musamman na sanya ido kan take hakkin dan adama a kasar Iran din zuwa tsawon shekara guda.
Qasemi ya ce, a ra'ayinsu, tsawaita shirin rahoton kare hakkin dan adam har na tsawon shekara guda abu ne da bai dace ba kuma bai kamata ba. (Ahmad Fagam)