Tunanin da aka kirkirowa al'umma
Tunanin Markisanci, kamar fitowar rana ce, wadda ke haskaka wata hanya da al'umma za ta yi amfani da ita wajen gano tarihin doka, da yadda al'umma za ta zabi hanyar 'yantar da kanta.
——Tunanin kimiyya: Ya nuna wa al'umma wata hanya ta samun 'yancin kansu
——Tunanin al'umma: Ya haska wata hanya madaidaiciya da za'a bi wajen ciyar da tarihi gaba, wato dogara da kokarin al'umma
——Tunanin aiwatarwa: Ba maganar ilimi a dakin karatu ba, ilimin da aka kirkiro da nufin canza makomar al'umma
——Tunanin dake tafiya da zamani: Yana zakulo sabbin hanyoyin da za'a bi wajen samun ci gaba, da magance sabbin kalubalolin da al'umma za su fuskanta