in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban ICPO: Algeria ta taka muhimmiyar rawa wajen kare zaman karkon yankin
2018-05-04 13:44:04 cri
Jiya Alhamis, shugaban kungiyar 'yan sandan masu binciken manyan laifuffuka ta duniya wato ICPO Meng Hongwei ya bayyana cewa, kasar Algeria ta taka muhimmiyar rawa wajen kiyaye yanayin zaman karko a yankin.

Mr. Meng ya bayyana haka ne bayan ganawarsa da ministan harkokin gida na kasar Algeria, inda ya kuma kara da cewa, hukumomin tsaron kasar Algeria sun ba da gudummawa matuka a fannonin yaki da manyan laifuffuka, kiyaye tsaro na kasar, har ma da yankin baki daya.

Haka kuma, ya ce, a halin yanzu, gamayyar kasa da kasa suna fuskantar kalubalolin tsaro da dama, da suka hada da ta'addanci, da aiwatar da laifuffuka bisa jagorancin kungiyoyi, da matsalar cin rani ba bisa doka ba, da kuma fasa kwauri da dai sauransu, lamarin da ke gurgunta yanayin zaman karko a yankin Asiya ta yamma, da Afirka ta arewa.

Sa'an nan, ya jaddada cewa, ya kamata kungiyar ICPO, ta karfafa hadin gwiwar dake tsakaninta da gwamnatocin kasa da kasa, domin fuskantar wadannan kalubaloli.

Bugu da kari, ya ce, babban makasudin ziyarar da ya kai Algeria shi ne, zurfafa mu'amalar dake tsakanin kungiyarsa da rundunar 'yan sandan kasar Algeria, ta yadda za a kara hadin gwiwar bangarorin biyu, wajen fuskantar kalubalolin da za a gamu da su a nan gaba. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China