in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Algeria ta ware ranakun makoki ga wadanda hadarin jirgin sama ya rutsa da su
2018-04-12 10:53:43 cri

Fadar shugaban kasar Algeria ta sanar a jiya Laraba cewa, ta ware kwanaki uku domin nuna juyayi ga mamatan da hadarin jirgin saman sojin kasar ya rutsa da su a wannan rana.

Shugaban kasar Abdelaziz Bouteflika ya jajantawa iyalan mamatan a cikin wata sanarwar da ya bayar a wannan rana, tare da sanar da ware kwanaki uku a matsayin ranakun makoki a fadin kasar. Ban da wannan kuma, jama'a za su yi bikin nuna juyayi a ranar Juma'a 13 da kuma yin addu'o'i ga mamatan a wannan lokaci.

An ba da labari cewa, da safiyar Laraba 11 ga wata ne, wani jirgin saman sojojin kasar mai sufurin kayayyaki ya fadi a gonaki dake dab da filin saukar jiragen sama na Boufarik dake lardin Blida jim kadan bayan da ya tashi sama, wanda ya kasance hadari mafi muni a tarihin kasar, kawo yanzu adadin mutanen da suka rasa rayuka ya riga ya kai 257. (Amina Xu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China