in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Algeria ta kammala wani babban sashi na titin da zai hade sassan Afirka
2018-04-24 10:03:11 cri
Mahukuntan kasar Algeria, sun ce sun cimma nasarar kammala ginin titin mota da zai hade wasu muhimman sassan nahiyar Afirka da juna. Kamfanin dillancin labarai na APS ya ce tuni Algeria ta kammala ginin kilomita 1,600 na wannan titi, yayin da ake ci gaba da aikin gina karin kilomita 200.

APS ya rawaito babban sakataren kwamitin dake lura da wannan aiki Mohamed Ayadi, a yayin zaman kwamitin na 68 da ya gudana a birnin Algiers na cewa, nan gaba kadan kasar za ta kammala tsagin ta na aikin gina wannan titi, wanda zai hade kasashen Algeria, da Tunisia, da Mali, da Nijar, da Najeriya da Chadi.

Da yake tsokaci game da aikin, ministan ayyuka da sufuri na kasar Algeria Abdelghani Zaalane, ya ce kasar sa na baiwa fannin samar da ababen more rayuwar jama'a cikakken muhimmanci, kasancewar sa muhimmin kashi na bunkasa tattalin arziki, da samar da ci gaba, tare da inganta cinikayya da zuba jari. Har ila yau aikin zai zamo muhimmin bangare na dukulewar nahiyar, zai kuma kara kyautata zamantakewar al'ummar nahiyar Afirka baki daya.

Cikin mahalarta taron da ya gudana a jiya Litinin, hadda wakilan hukumar tarayyar turai ta EU, da na bankin raya nahiyar Afirka, da bankin samar da ci gaba na kasashen musulmai ko IDB, da bankin kasashen larabawa don bunkasa ci gaban Afirka na BADEA.

Ana fatan kammalar bangaren kasar Algeria na wannan titi, wanda zai kai kilomita 4,500, zai bunkasa hada hadar cinikayya, da bunkasar musaya tsakanin sassan Arewaci zuwa yammacin nahiyar Afirka. (Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China