in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An hallaka yan ta'adda 5 a arewacin Algeriya
2017-02-16 10:08:13 cri
Ma'aikatar tsaron kasar Aljeriya ta ce, a jiya Laraba, dakarun tsaro masu yaki da ta'addanci a kasar sun yi nasarar kashe mayaka masu dauke da makamai su 5, kana sun kwace wasu makamai masu yawa daga hannun su a lardin Bouira, mai tazarar kilomita 110 a gabas birnin Algiers na kasar.

Sanarwar ta ce, an yi dauki ba dadin ne a babban dajin nan na Laadjiba dake Bouira, bayan da dakaru masu yaki da ta'addancin suka samu cikakken rahoto cewa yan ta'addan suna wancan wuri.

Dakarun tsaron sun yi arangama da mayakan masu dauke da makamai, a inda suka yi nasarar kashe 5 daga cikinsu, kana suka kwace manyan bindigogi masu sarrafa kansu da alburusai.

Sanarwar ta kara da cewa, har yanzu jami'an na cigaba da fatattakar mayaka masu dauke da makaman. (Ahmad)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China