in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministan harkokin wajen Algeria ya yi kira ga kasashen Bahar Rum da su tinkari matsalar bakin haure ba bisa doka ba
2018-01-22 10:55:48 cri
A Jiya Lahadi ne ministan harkokin wajen kasar Algeria Abdelkader Messahel ya ce, kamata ya yi kasashen dake mashigin Bahar Rum su karfafa hadin kai, don tinkarar matsalar bakin haure ba bisa doka ba tare.

Ministan ya bayyana haka ne a yayin taron manema lamaru da aka shirya bayan taron ministocin harkokin wajen kasashe 10 dake yammacin Bahar Rum, inda ya ce, wannan matsala ta dade tana addabar yankin, ga shi kuma yanzu ana fuskantar barazanar ta'addanci, saboda haka, ya kamata kasashen su hada kai, domin tinkarar kalubalen.

Ministan ya kuma jaddada cewa, muddin an gaggauta samun ci gaba, da warware matsalolin da suka shafi talauci, da rashin ayyukan yi, za a iya tinkarar batun bakin haure ba bisa doka ba da bangarori daban daban ke fuskanta. Kana ya yi kira ga bangarori daban daban da su yi shawarwari ba tare da bata lokaci ba, don tabbatar da ra'ayin bai daya da suka cimma.

Baya ga haka, ministan ya bayyana cewa, ministocin harkokin waje masu halartar taron sun kuma tattauna kan matakan kara daidaitawa da juna, don tinkarar 'yan ta'adda da suka komo kasashensu daga yankin Gabas ta tsakiya bayan da kungiyar IS ta sha kaye.

An shirya taron ministocin harkokin wajen kasashen 10 na yammacin Bahar Rum ne a ranar 21 ga wata a Algiers, babban birnin kasar Algeria, taron dake da taken "neman dauwamamman ci gaban tattalin arziki da al'umma don tinkarar kalubalen da ake fuskanta". (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China