Kamfanin dillancin labaran kasar na APS ya ruwaito ministan harkokin cikin kasar Noureddine Bedoui na cewa, kasar ta Aljeriya tana daukar 'yan gudun hijira da mutanen da rikici a kasashensu ya raba da muhallansu a matsayin bakin ta.
Bedoui ya ce, hukumomi na sane da halin da 'yan gudun hijirar ke ciki musamman mata da kananan yara, kuma gwamnati na duba yiwuwar samar wa 'yan gudun hijirar aikin yi, musamman a fannin gine-gine.
Daruruwan Dubban 'yan gudun hijira gilibi daga kasashen Nijar, Chadi, Mali da Syria da Libya ne ke zauna a cikin kasar Aljeriya, sakamakon yakin da ake gwabzawa a kasashensu.(Ibrahim)