in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan kasar Sin zai halarci taron shugabannin Sin, Japan da Koriya ta Kudu karo na 7
2018-05-03 10:49:05 cri

Jiya Laraba ne Hua Chunying, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta bayyana cewa, firaministan kasar Sin Li Keqiang zai halarci taron shugabannin kasashen Sin, Japan da Koriya ta Kudu karo na 7 da zai gudana a kasar Japan, lamarin da zai bude sabon babi na hadin gwiwa a tsakanin kasashen 3, da kuma ba da sabuwar gudummawa ga samun zaman lafiya, kwanciyar hankali, ci gaba da wadata a yankin da suke ciki.

A yayin taron manema labaru da aka saba shiryawa, madam Hua ta ce, hadin gwiwa da ke tsakanin Sin, Japan da Koriya ta Kudu, wani muhimmin bangare ne na hadin gwiwa a tsakanin kasashen gabashin Asiya. A cikin shekaru 19 da aka fara yin hadin gwiwa tsakanin kasashen 3, an kafa tsarin hadin gwiwa daga dukkan fannoni, inda aka ba taron shugabannin kasashen 3 muhimmanci matuka, tare da gudanar da tarukan ministoci 21 da tattaunawa fiye da 70 a matakai daban daban, sa'an nan an bude ofishin sakatariyar hadin gwiwa a tsakanin kasashen 3. Har ila yau kasashen 3 sun samu sakamako mai kyau a fannonin yin mu'amala da hadin gwiwa ta fuskar tattalin arziki da ciniki, hada-hadar kudi, sufuri, al'adu, ilmi, muhalli, kiwon lafiya, daidaita batutuwan da suka biyo bayan bala'i da dai sauransu. Sun kuma daddale yarjejeniyar zuba jari a tsakaninsu, tare da gudanar da shawarwari guda 13 kan yarjejeniyar yin ciniki cikin 'yanci a tsakanin kasashen 3. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China