Yau Talata a nan Beijing, Li Keqiang ya ce, kasar Sin ba za ta yunkura kara girmanta ba har abada, za ta maida hankali ne kan daidaita harkokinta.
Li ya kara da cewa, kasar Sin, kasa ce mai tasowa. Ba ta da yunkurin kara girmanta. Koda a nan gaba ta bunkasa, amma ba za ta ci zalin sauran kasashen duniya ba. Tana son raya hulda a tsakaninta da sauran kasashe bisa ka'idar girmama juna da yin zaman daidai wa daida da cin moriyar juna, a kokarin raya al'umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil'Adama.
Ya ci gaba da cewa, kasar Sin tana kiyaye cikakkun yankunanta, ba kuma za ta yarda da raba wani yanki daga jikinta ba. Duk da haka, ba za ta mamaye sauran yankuna ba. Kasar Sin tana bin hanyar samun ci gaba ne ta hanyar lumana. (Tasallah Yuan)