in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ya kamata a neman ci gaban zaman takewar al'umma cikin yanayin adalci, in ji firaministan Sin
2018-04-28 11:14:31 cri
Jiya Jumma'a, majalisar gudanarwar kasar Sin ta kira taron binciken ayyuka karo na farko, inda firaministan kasar Li Keqiang ya ba da jawabi cewa, ya kamata gwamnatoci da hukumomin kasar su gudanar da ayyukansu bisa tsarin gurguzu na musamman na Sin a karkashin jagorancin shugaba Xi Jinping, a gaggauta ayyukan yin kwaskwarima da kuma kiyaye yanayin adalci yadda ya kamata.

Haka kuma, Mr. Li ya ce, cikin shekaru biyar da suka gabata, gwamnatocin kasar su dukufa wajen gudanar da bincike kan ayyukansu bisa bukatun Jam'iyyar Kwaminis ta Kasar Sin, yayin da samun babban ci gaban a fannin yaki da cin hanci da karbar rashawa. A nan gaba kuma, za a ci gaba da mai da hankali kan wadannan ayyuka, ta yadda za a samar da hidima ga al'ummar kasa yadda ya kamata. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China