in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan kasar Sin ya nemi ra'ayoyin jama'a game da daftarin rahoton aikin gwamnati
2018-02-02 09:46:13 cri

A jiya Alhamis ne firaministan kasar Sin Li Keqiang ya shugabanci wani taron karawa juna sani don tattaunawa da wakilai daga bangarorin ilimi, kimiyya da fasahar kere-kere, da al'adu da lafiya, wasanni, har ma da bangaren fararen hula don jin ra'ayoyinsu game da daftarin rahoton aikin gwamnati.

Wakilai guda tara sun gabatar da nasarorin da aka cimma a cikin rahoton aikinsu, suka kuma gabatar da shawarwari kan yadda za a inganta rahoton.

Bayan ya tattauna da wakilai, Firaminista Li ya yi amfani da wannan dama wajen mika gaisuwar murnar bikin bazara bisa kalandar gargajiyar kasar Sin dake tafe, inda ya yi kira da a kara ba da shawarwari kan yadda za a inganta aikin gwamnati.

Firaminista Li ya ce , ya kamata gwamnatoci a dukkan matakai su karfafa samar da daidaito a bangarorin ilimi da yanayin karatu, sannan su taimakawa ci gaban gina makarantun gwamnati da ma masu zaman kansu.

Ya kara da cewa, akwai bukatar gwamnati a nata bangaren ta inganta aikinta ta hanyar tattaunawa da jama'a a kai- a kai.

Shi ma da yake jawabi shugaban jami'ar Wuhan dake nan kasar Sin Dou Xiankang, ya bayyana fatan cewa, gwamnati za ta rika taimakawa masana kan irin rawar da suke takawa ta yadda za a gina jami'o'i masu inganci a yankunan tsakiya da yammacin kasar. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China