in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Li Keqiang da Li Zhanshu sun gana da shugaban kasar Namibia
2018-03-30 20:42:40 cri
Firaministan kasar Sin Li Keqiang, da shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin Li Zhanshu, sun gana da shugaban kasar Namibia Hage Gottfried Geingob a yau Jumma'a a nan birnin Beijing.

A yayin ganawar, Li Keqiang ya bayyana cewa, Sin tana fatan zurfafa imani kan harkokin siyasa, da hadin gwiwar samun moriyar juna, da kara yin mu'amala da juna kan harkokin yankunan kasa da kasa, da raya dangantakar dake tsakanin kasashen biyu. Ya ce Sin tana son yin hadin gwiwa tare da kasar Namibia kan tsare-tsaren samun bunkasuwa, da hadin kan a wasu muhimman fannoni, da nuna goyon baya ga tsarin tattalin arzikin duniya na bai daya, da yin ciniki da zuba jari cikin 'yanci da sauki. Sauran sun hada da kin amincewa da ra'ayin bada kariya ga cinikayya, domin ta haka ne za su samu bunkasuwa tare da cin moriyar juna.

A yayin ganawar, Li Zhanshu ya yi nuni da cewa, majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, na fatan ci gaba da kokari tare da majalisar dokokin kasar Namibia, wajen aiwatar da ayyukan da shugabannin kasashen biyu suka cimma daidaito a kan su, da kara sada zumunta da juna, da nuna goyon baya ga dandalin tattaunawa kan hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka, da hadin gwiwar dake tsakanin sassan bisa jagorancin shawarar "ziri daya da hanya daya".

A nasa bangare, shugaba Geingob ya jinjinawa manufofin Sin ga kasashen Afirka. Ya ce, dangantakar dake tsakanin kasashen biyu ta bunkasa zuwa matsayin dangantakar abokantaka ta hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare a dukkan fannoni, kuma kasar Namibia tana fatan zurfafa hadin gwiwar dake tsakaninta da kasar Sin a fannoni daban daban, da nuna goyon baya ga mu'amala a tsakanin hukumomin kafa dokokin kasashen biyu, da kuma sa kaimi ga raya dangantakar dake tsakanin kasashen biyu. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China