Li ya nuna cewa, takaddamar cinikayya da ake yi, zai yi mummunan tasiri ga farfadowar tattalin arzikin duniya, kana, zama a tattauna ita ce hanya daya tilo da za'a iya bi wajen warware takaddamar. Kasar Sin za ta kara aiwatar da manufar yin gyare-gyare a gida da bude kofarta ga kasashen waje, haka kuma tana fatan kasashe daban-daban za su ci gajiyar wannan manufa. (Murtala Zhang)